Ƴan bindiga a jihar Zamfara suna tilasta wa mazauna kauyuka biyan harajin da suka kakaba musu na noma

0 201

Yan bindiga a jihar Zamfara sun sake daukar wani mataki na rashin tausayi domin tilasta wa mazauna kauyukan biyan harajin da suka kakaba musu na noma.

Mazauna yankunan da lamarin ya shafa sun shaida wa manema labarai cewa, a yanzu ‘yan bindigar suna kona amfanin gona da ba a girbe ba a gonakinsu, saboda rashin biyan harajin da suka kakaba musu.

Wasu mazauna garin Magami da ke da tazarar kilomita 50 kudu da Gusau babban birnin jihar, sun shaida wa wakilinmu cewa barayin sun kona wata gonar masara mallakar wani mai suna Alhaji Dankoli.

A garin Kanoma wani Birni dake karamar hukumar Maru a jihar, ‘yan fashin dajin sun saka harajin naira miliyan 8.

An bayyana cewa duk da katsewar hanyoyin sadarwa a jihar Zamfara, har yanzu ‘yan bindiga na kai hare-hare a cikin al’umma tare da yin garkuwa da mutane tare da kakaba harajin noma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: