Gwamna Badaru Abubakar ya ce a kullum da tausayin talaka Shugaba Buhari yake kwana yana tashi a ransa

0 94

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar, na Jihar Jigawa, ya ce a kullum da talaka Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yake kwana ya tashi a ransa.

Gwamnan, wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin zabukan fidda gwani na Gwamnonin APC ya bayyana hakan ne a cikin shirin siyasa na Politics Today na gidan talabijin na Channels.

Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar ya ce, shugaban Kasa yana gudanar da ayyukan gwamnatinsa tsakani da Allah. Kuma a kodayaushe yakan kwana ya kuma tashi da talaka a ransa; tare da tunanin ta ya ya zai inganta rayuwar shi.

Gwamna Badaru ya kuma ce yana da yakinin cewa ko a babban zabe mai zuwa na shekara ta 2023, ’yan Najeriya za su sake zabar APC saboda sun san irin ta’asar da PDP ta yi a baya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: