Labarai

Kimanin mutane 7 ne aka bada rahotan cewa yan bindiga sun kashe a garin Faru na karamar hukumar Maradun ta Jihar Zamfara

Kimanin mutane 7 ne aka bada rahotan cewa yan bindigar sun kashe a garin Faru na karamar hukumar Maradun ta Jihar Zamfara.

Wannan na zuwa ne kwanaki 2, bayan yan bindigar sun kashe mutane 48 a karamar hukumar Bakura ta Jihar.

Da ya ke zantawa da gidan Talabijin na Channels Tv, wani shaidar gani da ido ya ce sun kewaye garin Faru a jiya Lahadi da Rana.

A cewarsa, yan bindigar sun kewaye garin ne da misalin karfe 2 na Dare, inda suka din ga harbi kan mai uwa da wabi.

Shima wani shaidar gani da Ido ya tabbatar da mutuwar mutane 7 a garin, inda ya kara da cewa mutane da dama sun samu raunika a lokacin.

Kawo yanzu rundunar yan sandan Jihar ba ta ce komai ba kan kaiwa hare-haren.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: