Labarai

Jinkirin da ake samu a lokacin loda man fetur a shine dalilin da ya saka ake samun cunkuso a gidajen mai – NNPC

Kamfanin Rarraba Arzikin Man fetur NNPC ya ce jinkirin da ake samu a lokacin loda man fetur a cibiyar Kamfanin, shine dalilin da ya saka ake samun cunkuso a gidajen man fetur na Abuja.

Cikin karshen makon nan ne ake samun cunkuson motoci a gidajen man fetur a sassan birnin tarayya Abuja.

Da yake jawabi ga manema labarai cikin wata sanarwa, Kakakin Kamfanin Garba Deen Muhammad, ya ce siyan man fetur din da ma’aikatan gwamnati suka yi bayan dawowa daga hutun Sallah.

Sanarwar ta ce ana samun jinkirin ne a gidajen man fetur din ne, biyo bayan yadda aikin Jigilar ya ke jan kafa.

Haka kuma Kamfanin na NNPC ya ce ya na yin duk mai yuwuwa domin magance matsalar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: