Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na jihar Jigawa ya aike da sakon ta’aziyya ga mai martaba sarkin Kazaure Alhaji Najib Hussaini Adamu bisa rasuwar Tafidan Kazaure Alhaji Iliyasu Adamu.

A sakon ta’aziyyar mai dauke da sa hannun mai bashi shawara kan kafafan yada labarai da hulda da jama’a, Habibu Nuhu Kila, gwamnan ya bayyana rasuwar marigayin a matsayin babban rashi ba ga masarautar Kazaure ko jihar Jigawa kadai ba, har ma ga kasarnan baki daya da kuma sauran alummar musulmi.

Gwamnan ya kuma bayyana marigayi Tafidan Kazaure Alhaji Iliyasu Adamu a matsayin gogaggen ma’aikaci, shugaban al’umma da ya himmatu wajen yiwa al’umma hidima da kuma kawo sauye sauye ga al’umma.

Daga nan sai ya yi adduar Allah ya ji kansa ya kuma baiwa iyalai da ‘yan’uwa hakurin jure rashinsa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: