Gwamna Badaru ya bayyana shugaba Buhari a matsayin mutum mai gaskiya da riƙon amana

0 248

Gwamna Muhammad Badaru, na Jihar Jigawa ya bayyana cewa shugaba Buhari mutum ne mai gaskiya da riƙon amana wanda yake kwanciya bacci da yan Najeriya a zuciyarsa.

Gwamna Badaru Abubakar ya ce shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi abubuwa da dama ga yan Najeriya ta ɓangaren kyautata rayuwarsu da kuma cigaban tattalin arziƙi da walwala.

Gwamnan ya kuma yaba wa Buhari bisa tsare-tsaren da ya ƙirƙiro wajen haɓɓaka tattalin arziƙi, musamman ta fannin gyara ɓangaren noma a ƙasar nan.

Gwamnan yayi wannan jawabai ne a wurin taron ƙarbar Graxe Bent, tsohon sanata mai wakiltar Adamawa ta kudu, wanda ya fice daga PDP zuwa APC ranar Asabar a Yola. Shugaban kwamitin riƙo na jam’iyyar APC, Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe, wanda tsohon shugaban majalisar Dattijai ta kasa, Sanata Ken Nnamani, ya wakilta, ya ce za’a dama da Sanata Bent kamar yadda ake yiwa kowane mamban APC.

Leave a Reply

%d bloggers like this: