Wasu da ake kyautata zaton yan Fashi da Makami ne sun kashe wani Matashi dan shekara 25 mai suna Adamu Abdullahi a kyauyen Gasakole na karamar hukumar Ringim ta jihar nan.

Mutanen garin sun fadawa manema labarai cewa wasu Fulani ne suka kira Matashin a waya wanda yake yin Achaba, domin ya dauke su zuwa kyauyen Marawa.

Sai dai daga baya ne a kaga gawar Matashin cikin jini akan hanyar Jirgin Kasa, tare da raunika a jikinsa, kuma barayin sunyi awun gaba da Babur din nasa.

Kakakin rundunar yan Sandan Jihar Jigawa ASP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

A cewarsa, tuni aka garzaya da matashin zuwa Asibitin Murtala dake Kano, sai dai ya mutu a lokacin da yake karbar magani.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: