Adadin mutanen da cutar Corona ta hallaka a Najeriya ya karu zuwa dubu 2,124, biyo bayan samun karin mutane 2 da cutar ta hallaka a jiya Lahadi.

Cibiyar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa wato NCDC, ita ce ta bayyana hakan a shafinta na Facebook, inda ta ce mutane 12 ne kacal suka sake kamuwa da cutar a jiya a Najeriya baki daya.

NCDC, ta ce an samu 6 Akwa Ibom, 4 Ogun da kuma 2 a jihar Rivers sai dai kuma Jihar Legas ba’a samu mutum guda daya kamu da cutar ba a jiya Lahadi sabanin yadda aka saba gani.

Cibiyar ta NCDC ta ce kawo yanzu, kimanin mutane dubu 156,439 ne suka warke daga cibiyoyin kula da su, haka kuma akwai mutane dubu 2,000 da suke cigaba da samun kulawar likitoci a cibiyoyin.

Kawo yanzu, kimanin mutane Miliyan 2 da dubu 300 ne aka musu gwajin cutar a kasa baki daya tun bayan bayyanarta a watan Fabreru na shekarar 2020.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: