Gwamna Badaru Ya Kaddamar Da Hanyar Ringim – Bachawa – Doko

0 81

Gwamna Badaru Abubakar ya kaddamar da hanyar Ringim zuwa Bachawa zuwa Doko wanda aka gina akan sama da Naira miliyan dubu 3 da miliyan 800.

Gwamnan ya kuma kaddamar da titunan cikin garin Ringim mai tsawon sama da kilomita hudu da kuma titunan cikin garin Sabongarin ‘Ya’ya kashi na 2.

Kaddamar da ayyukan na daga cikin abubuwan da ake gudanarwa na karshen wa’adin mulkinsa na Gwamnan Jihar.

A wani labarin makamancin haka, Gwamnan ya gudanar da bikin bude kwalejin JICORAS ta jihar Jigawa dake Babura da kwalejin kimiyyar jinya dake Babura.

Da yake jawabi a wajen bikin, Gwamna Badaru Abubakar ya ce kwalejojin za su taimaka wajen horas da karin jami’an kiwon lafiya tare da inganta harkokin kiwon lafiya a fadin jihar. Gwamnan ya kuma kaddamar da hanyar Koko zuwa Fayam-Fayam wanda aka gina akan kudi sama da naira miliyan dubu biyar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: