Wasu Masu Yiwa Kasa Hidima Su 5 Za Su Maimaita Shekarar Hidimar Su A Jihar Bauchi

0 88

Ko’odinetar hukumar matasa masu yi wa kasa hidima ta kasa NYSC reshen jihar Bauchi, Rifkatu Yakubu, ta ce wasu masu yiwa kasa hidima su 5 ‘yan rukunin B kashi na 1 na shekarar 2022, za su maimaita shekarar hidimar su a jihar.

Ta bayyana hakan ne a jiya ga Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa a Bauchi, a yayin bayar da takardar shaidar kammala bautar kasa ga wadanda suka yiwa kasa hidima.

Rifkatu Yakubu ta ce an hukunta wadanda lamarin ya shafa ne bisa laifuka daban-daban da suka hada da tserewa da kuma rashin zuwa aiki a shekararsu ta yiwa kasa hidima.

Ta sake nanata cewa hukumar bata wasa ko kadan ga batun kin zuwa aiki kuma ba za ta yi shakkar hukunta duk wani mai yiwa kasa hidima da ya sabawa doka ba.

Sai dai ta yi kira ga masu yiwa kasa hidima da suka kammala da su tafi kai tsaye zuwa gidajensu su hadu da iyayensu da ‘yan uwansu, inda ta hore su da su guji tafiya cikin dare.

Masu yiwa kasa hidima su 747 ne suka kammala hidimtawa kasa a jihar Bauchi kuma an ba su takardar shaidar yi wa kasa hidima.

Leave a Reply

%d bloggers like this: