Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Gombe, Sa’adu Adamu, a jiya ya ce maniyyata dubu 2 da 556 ne za ayi jigilarsu zuwa Saudiyya daga Gombe ta jirgin saman Air Peace a bana.
Sa’adu Adamu ya shaida wa manema labarai a Gombe cewa a ranar 3 ga watan Yuni ne ake sa ran za a fara jigilar rukunin farko, kuma za ayi sawu kusan tara kasancewar jirgin karami ne.
A cewarsa, hukumar ta zabi kamfanin jirgin ne saboda an tabbatar da cewa sabon kamfanin ne tare da fatan za a kammala jigilar maniyyatan a cikin kwanaki taran.
Ya ce biyo bayan sake gine-ginen da ake yi a kasar Saudiyya, an canza matsugunin da ake amfani da shi wajen saukar masu aikin hajji, inda aka samu wasu wuraren amma a yankin da tsohon masaukin yake.
Sa’adu Adamu ya ce hukumar ta yanke shawarar cigaba da kama masauki a yankin saboda jihar ta saba da wajen, a saboda haka aka yi kokarin ganin an samar da masauki a wajen ga mahajjatan.