Gwamna Badaru yace nan da yan makonni kadan za a saki wutar lantarki daga Gagarawa domin amfanin alummar masarautar Gumel

0 67

Gwamnan Jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar yace nan da yan makonni masu zuwa za a saki wutar lantarki daga babbar tashar lantarki ta Gagarawa domin amfanin alummar masarautar Gumel da wasu kananan Hukumomi.

Gwamnan ya sanar da hakan ne a sakon da ya aike dashi wajen bikin sallar Gani na masarautar Gumel.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Mallam Umar Namadi ya bayyana cewa samun hasken wutar lantarkin zai bunkasa tattalin arzikin alummar jihar Jigawa.

Gwamnan ya kara jaddada godiyarsa ga mai martaba Sarkin Gumel Alhaji Ahmed Muhammad Sani da Gumulawa bisa hadin kai da goyan bayan da suke bawa gwamnati wajen gudanar da ayyukanta.

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar yace gwamnatin jiha zata cigaba da bada gudunmawa domin inganta rayuwar alummar jihar nan yayinda gwamnati zata cigaba da yin ayyukan da zasu kawo cigaban tattalin arzikin alumma da jihar nan baki daya.

Gwamnan ya kuma taya Gumulawa murnar bikin sallar Gani ta bana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: