Sheik Ahmed Gumi ya gargadi gwamnatin tarayya kan yunkurin ayyana yan bindiga a matsayin Yan Ta’adda

0 80

Malamin Addinin Islaman nan mazaunin Jihar Kaduna Mai Yawan Jawo Cece-Kuce Sheikh Ahmed Gumi ya gargadi gwamnatin tarayya kan yunkurin ayyana yan bindiga a matsayin Yan Ta’adda, inda ya ce hakan yana da hadari.

Ana Cigaba da yin kiraye-kiraye a sassan Kasar nan kan gwamnatin tarayya ta ayyana yan Bindiga a matsayin yan Kungiyar Ta’adda.

Tun farkon watan nan, Majalisar Wakilai da ta Dattawa da kuma Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i sun bukaci gwamnatin tarayya ta ayyana yan bindigar a matsayin yan Ta’adda.

Sai dai Gumi wanda ya sha bukatar yan bindigar su ajiye Makaman su, ya ce ayyana su a matsayin yan ta’adda, zasu cigaba da zafafa kaiwa hare-haren su.

Cikin wani Rubutu da ya wallafa a shafin sa na Facebook, Sheikh Gumi, ya ce ayyana yan bindiga a matsayin yan Ta’adda zai saka yan ta’addar kasashen waje su shiga cikin su.

A cewarsa, Yankin Arewa Maso Gabas, na cigaba da fuskantar hare-haren yan ta’adda tsawon shekaru 12, inda yace matukar yan Najeriya suka bari yan ta’adda suka shiga cikin yan bindiga, yankin Arewa Maso Yamma  zai zama tamkar takwarar sa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: