Gwamna Bauchi Bala Mohammed Ya Sallami Kwamishinan Harkokin Tsaro Na Cikin Gida

0 301

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya sallami Kwamishinan Harkokin Tsaro na Cikin Gida, Alhaji Ibrahim Gambo Galadima, daga muƙaminsa.

An bayyana hakan ne cikin wata gajeriyar sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin yaɗa labarai, Kwamared Mukhtar Gidado, ya sanya wa hannu, wadda aka fitar da ita ga manema labarai a safiyar Litinin.

A cewar sanarwar, matakin na daga cikin wani sauyi kaɗan da gwamnan ya amince da shi a cikin majalisar zartarwar jihar, inda aka cire Galadima daga muƙaminsa nan take.

Gwamnatin ta ce ana ɗaukar irin wannan mataki ne lokaci zuwa lokaci domin kawo sabbin dabaru, ƙarfafa shugabanci, da inganta ayyukan gwamnati.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “A bisa wannan mataki, an sallami Kwamishinan Harkokin Tsaro na Cikin Gida da Al’amuran Cikin Gida, Alhaji Ibrahim Galadima, daga matsayin mamba a majalisar zartarwar jihar.

Mai magana da yawun gwamnan ya bayyana cewa matakin ya dace da kudurin gwamnati na duba tsarin majalisar zartarwa lokaci zuwa lokaci, domin kawo sabbin dabaru, ƙarfafa shugabanci, da inganta aiwatar da manufofi da shirye-shiryen gwamnati a fadin jihar.

Gwamna Bala Mohammed ya yabawa Galadima bisa gudunmawar da ya bayar a lokacin da yake kan muƙamin, tare da yi masa fatan alheri a rayuwarsa ta gaba, yana mai jaddada kudurin gwamnatinsa na tabbatar da zaman lafiya, tsaro da kyakkyawan shugabanci a Jihar Bauchi.

Leave a Reply