Iyalan Mamatan da Aka Kashe A Uromi Sun Ce Har Yanzu Gwamnatin Edo Ba Ta Biya Su Diyya Ba

0 213

Gwamnatin Jihar Edo na fuskantar suka, bayan da iyalan waɗanda aka kashe a kisan gillar Uromi suka ce har yanzu ba a biya su diyya ba, duk da cikar watanni goma sha ɗaya da faruwar lamarin daya girgiza al’umma.

A ranar 28 ga Maris, 2025, wasu mafarauta 16 da ke kan hanyarsu daga Jihar Rivers zuwa Kano domin bukukuwan Sallah, sun rasa rayukansu bayan da ‘yan sa-kai da wasu matasa dauke da makamai suka kai musu hari a Jihar Edo.

Rahotanni sun ce maharan sun tare motar da mafarautan ke ciki a kan hanyar Uromi zuwa Obajana, a Karamar Hukumar Esan North-East, inda suka fitar da su daya bayan daya, suka doke su, sannan suka kona su da ransu, bisa zargin cewa masu garkuwa da mutane ne.

Wadanda aka kashe ‘yan asalin garin Torankawa ne da ke Karamar Hukumar Bunkure a Jihar Kano. Bayan faruwar lamarin, Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya yi alkawarin biyan diyya ga iyalan mamatan, a lokacin da ya kai ziyarar jaje tare da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.

Sai dai kusan shekara guda bayan wannan alkawari, iyalan mamatan sun ce ba su karɓi ko sisin kwabo ba. Sun bayyana cewa duk da alkawuran da aka yi, babu wani abu a zahiri da aka yi domin rage radadin da suke ciki.

Daya daga cikin wadanda lamarin ya shafa shi ne Ibrahim Isa, mai shekara 45, wanda shi kaɗai ya tsira daga harin. Mahaifine ga yara shida, kuma ya ce yana fama da radadi tun bayan dawowarsa, inda ya ce har yanzu babu wani tallafi da ya samu duk da alkawuran da aka yi masa.

A martaninsu, gwamnatin Kano ta ce ba za ta bari a manta da batun ba, inda iyalan mamatan suka ce jinkirin cika alkawuran na kara jefa su cikin bakin ciki, tare da haifar da tambayoyi kan adalci da gaskiya.

Leave a Reply