Gwamna Ganduje ya bada Sandar sarauta ga Mai Martaba Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado-Bayero

0 80

Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya bada Sandar Sarauta da Mai Martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado-Bayero, wanda shine a matsayin Sarki na biyu a jihar.

Masarautar Bichi tana daya daga cikin sabbin Masarautu da Gwamnatin Gwamna Ganduje ta kirkira.

Sauran Masarautun sune Rano, Gaya and Karaye, kari akan wanda ake da ita ta birnin Kano.

Da yake Jawabi bayan mikawa Sarkin sandar Gwamna Ganduje, ya ce gwamnatinsa ta yanke hukuncin kara adadin Masarautun biyo bayan gudunmawar da suke bayarwa wajen cigaba tun daga tushe.

Haka kuma ya bukaci Sarkin da sauran Sarakunan Jihar su cigaba da tallafawa kokarin gwamnati a yakin da take yi na kare rayuka da Duniyoyin Al’umma.

 A jawabinsa na karbar Sandar girman, Sarkin na Bichi ya yi Alkawarin yin adalci ga mutanen da suke Masarautar.

Kazalika, ya bukaci mutanen Masarautarsa, su cigaba da kokarin ganin sun sanya yayansu a Makarantu domin samun Ilimi mai Nagarta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: