Civil Defence reshen Jihar Kaduna ta kammala horas da Jami’anta Mata 54 a jihar

0 167

Rundunar Hukumar Tsaro ta Farin Kaya wanda akafi sani da Civil Defence reshen Jihar Kaduna ta kammala horas da Jami’anta Mata 54 a jihar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN, ya rawaito cewa kimanin Jami’an hukumar Mata 54 ne aka basu horo ta yadda zasu samar da tsaro ga kadarorin gwamnati da kuma Makarantun da aka tura su.

Ministan Ma’aikatar Harkokin Mata Mista Rauf Aregbesola, shine ya karbi faretin girmamawa daga Matan wanda akayi a Kwalegin Horas da Jami’an Hukumar Lura da Gidajen Gyaran Halayya dake Kaduna.

Ministan wanda Mataimakin Daraktan Hukumar Kula da rundunonin Civil Defence da hukumar kashe gobara da hukumar shige da fice da kuma hukumar gyaran halayya Malam Abdullahi Salihu, ya wakilta, ya bayyana zabar matan a matsayin abinda ya dace.

Kazalika, ya ce manufar horas da Matan shine domin su dakile hare haren yan bindiga da suke kaiwa Makarantu da sauran wurare.

Leave a Reply

%d bloggers like this: