An raba Naira Biliyan 760 da Miliyan 717 ga gwamnatin tarayya da jihohi da kananan hukumomi

0 119

Asusun Rabon Arzikin Kasa ya raba Naira Biliyan 760 da Miliyan 717 ga bangarorin Gwamnati 3 wanda suka hada da gwamnatin tarayya da gwamnatocin Jihohi da kuma na kananan hukumomi a watan Yuli.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da aka fitar bayan kammala taron rabon arzikin wanda akayi ta bidiyon kai tsaye.

Sanarwar ta ce kudaden sun kunshi Naira Biliyan 617 da Miliyan 705 na kudaden Haraji, da kuma karin kudaden Harajin Kaya da akayi na Naira Biliyan 140 da Miliyan 555.

Daga cikin kudaden Harajin gwamnatin tarayya ta karbi Naira Biliyan 321 da Miliyan 226 a matsayin kasonta, sai kuma Jihohi da aka raba musu Naira Biliyan 222 da Miliyan 514, yayin da kananan hukumomin kuma aka raba musu Naira Biliyan 166 da Miliyan 562.

Kazalika an raba Naira Biliyan 50 da Miliyan 415 na kaso 13 cikin 100 ga hukumomin da suke da ruwa da tsaki da tara kudaden duk cikin wannan watan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: