Gwamnatin tarayya ta ce bazata gurfanar da tubabbun yan kungiyar Boko Haram a gaban kotu ba

0 99

Gwamnatin tarayya ta ce bazata gurfanar da tubabbun yan Kungiyar Boko Haram a gaban Kotu ba, saboda hakan ya sabawa dokar ayyukan yaki da ta’addanci na Duniya.

Ministan Yada Labarai na Kasa Alhaji Lai Muhammad, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da manema labarai a birnin Washington DC na Amurka.

Alhaji Lai Muhammad, ya ce gurfanarwa ko kuma kashe tubabbun Mayakan kungiyar Boko Haram, maimakon yi musu afuwa, ya sabawa abubuwan da kasashen Duniya sukeyi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN, ya rawaito cewa Ministan ya ce rundunar Sojin Najeriya sun fada masa cewa dokokin yaki na Duniya sun bayyana cewa duk yan ta’addar da suka mika wuya ana masu kallon Fursinan yaki.

A cewarsa, Sojojin Najeriya basu da hurumin Harbin tubabbun Yan Kungiyar Boko Haram, saboda suna daga cikin mutanen da Kungiyoyin Fararen Hula da Duniya, suka basu kariya a matsayin Fursunonin Yaki, inda ya kara da cewa dole a sauya musu tunani tare da mayar da su cikin Al’umma.

A yan kwanakin nan ana samun Mayakan Boko Haram da suke mika wuya ga Sojin Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: