NCDC ta tabbatar da cewa kimanin mutanen 304 ne suka harbu da cutar Corona

0 110

Cibiyar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa NCDC ta tabbatar da cewa kimanin mutanen 304 ne suka harbu da cutar Corona a jihohi 12 da suke Najeriya ciki harda babban birnin tarayya Abuja.

NCDC ta ce an samu sabbin mutane 3 da cutar ta hallaka a jiya Juma’a biyo bayan harbu da ita.

Cibiyar ta ce Jihar Rivers ce take da mutane masu yawa fiye da ko’ina Rivers 154 sai Ekiti 33, Edo da Abuja masu 20 and 18.

Sauran Jihohin sune Oyo – 17, Cross River – 15, Delta – 15, Akwa Ibom – 13, Ogun – 11, Bayelsa – four, Sokoto – two, Gombe – one, and Nasarawa – one.

Daga watan Fabreru na shekarar 2020, zuwa yanzu kimanin mutane dubu 185,571 ne suka harbu da cutar daga cikin mutane Miliyan 2 da dubu 648 da 684 da aka musu gwajin cutar a kasa baki daya.

Kawo yanzu kimanin mutane dubu 168,124 ne suka warke daga cutar baki daya, yayinda kuma aka samu rasuwar mutane dubu 2,247 da cutar ta hallaka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: