Rundunar Yan Sandan Jihar Jigawa ta kama mutane 2 bisa zargin su da aikata laifin satar Shanu

0 142

Rundunar Yan Sandan Jihar Jigawa ta kama mutane 2 bisa zargin su da aikata laifin satar Shanu a karamar hukumar Kafin Hausa.

Kakakin hukumar ASP Lawan Shiisu Adam, shine ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Dutse.

A cewarsa, mutanen su 5 sunje rigar Sabon Sara ce ta karamar hukumar Kafin Hausa da misalin karfe 4:30 na dare, tare da sace Shanu 2 na yankin.

ASP Lawan Shiisu, ya ce bayan matasan yankin sun bibiyi mutanen, shine suka gudu suka bar shanun, sai dai ya ce Matasan sunyi nasarar kama 2 daga cikin Barayin, yayinda kuma 3 suka tsere.

Kakakin rundunar ya ce mutanen da aka kama din sun hada da Aliyu Muhammad dan shekara 26 da kuma Danjummai mai shekara 25 kuma dukkanin su yan nan cikin garin Hadejia ne.

ASP Lawan Shiisu, ya ce Matasan da suka biyo barayin sun kone wata Mota wanda Barayin suka kuduri aniyar sake shanun a ciki.

Kazalika, ya ce suna cigaba da zurfafa bincike domin kamo sauran mutane 3 da suka tsere.

Leave a Reply

%d bloggers like this: