Wanda ake zargi da shigar da kwayoyi gidan yari a Kano shigo hannu

0 118

Hukumar gidajen yari a Najeirya ta ce ta kama daya daga cikin ma’aikatan da ke da hannu a shigarwa da daurarun miyagun kwayoyi da wayoyi cikin gidan gyaran hali na kurmawa da ke jihar Kano.

Hukumar tace ta gano shi ne bayan kafa wani kwamitin bincike da ya sanya ido kan ma’aikacin bayan da fursunoni suka yi yunkurin tserewa a ranar alhamis, din makon da ya gabata.

A cewar hukumar reshen jihar Kano, Sunan ma’aikacin nata Aminu Ibrahim, da ake zarginsa da kai wa wadan da aka yankewa hukuncin kisa da ke daure a gidan na kurmawan kayayyakin da aka haramta shiga da su.

Ta ganoo yunkurin nasa ne bayan da ya je bakin gidan makama inda ya karbo kwayoyin da wayoyi wanda ke dauke da sunayen wadanda za a bai wa su.

An karbe kayan da ya karbo da suka hada da wayoyin da wasu miyagun kwayoyin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: