Gwamnonin Najeriya sun karyata cewa an rabawa musu Naira Biliyan 243.8 daga cikin kudaden Paris Club

0 61

Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta karyata labarin da ke cewa an rabawa Jihohin Kasar nan Naira Biliyan 243.8 a watan Agusta daga cikin kudaden Paris Club.

Sakatariyar Kungiyar ce ta fitar da wannan sanarwar mai dauke da sahannun Shugaban Sashen Yada Labarai da Hulda da Jama’a Abdulrazaque Bello-Barkindo a Abuja.

Bello-Barkindo, ya bayyana zargin a matsayin kanzon kurege, wanda bashi da tushe balle makama daga marubucin sa.

Sanarwar ta ce Kudaden Paris Club ba a ajiye yake ba, ta yadda gwamnatin tarayya zata rika rabawa jihohi a duk lokacin da suka bukata.

A cewarsa, Paris Club kudade da suke ake bawa Jihohin da suke bin bashi, kuma ake dawowa dashi.

Kazalika, ya bukaci masu yada labarai su janye labarin da bashi da tushe balle makama, musamman abinda ya hada da maganar kudade a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: