Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya nemi janye karar da ya shigar kan mawallafin jaridar Daily Nigerian, Jaafar Jaafar, bisa bidiyon da ya wallafa dake nuna gwamnan yana karbar cin hanci.

Sai dai, majiyoyi na cewa zai janye karar ne domin samun damar shiga da wata sabuwar kara akan Jaafar Jaafar.

Gwamna Gunduje ya shigar da karar mawallafin bisa bidiyon da ya wallafa a shekarar 2018 wanda aka kama Gwamnan na zura dalolin Amurka cikin aljihun sa, da ake zargin ya karba daga hannun wani dan kwangila.

Ganduje, a sabuwar bukatar da ya mika, ya bukaci babbar kotun jihar Kano da kada ta cigaba da sauraron karar amma bai bayar da dalilinsa ba.

Majiyoyi sun ce Ganduje na shirin gabatar da sabuwar kara tare da sabbin masu shaida, kasancewar ya tsige daya daga cikin masu shaida na ainihi.

Tsohon hadimin Ganduje, Salihu Tanko Yakasai, na daga cikin masu shaidar Ganduje na farko a karar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: