Gwamna Badaru yace jihar Jigawa tana fuskantar kalubale daban-daban

0 122

A wani bikin da aka gudanar yau a Dutse, Gwamna Badaru yace jihar Jigawa na fuskantar kalubale daban-daban.

Yace majalisun kananan hukumomi a jiharnan sun samu cigaba sosai karkashin manufofin cigaba, duk da kalubalen tattalin arziki da na jin dadin mutane da jihar ke fuskanta.

Gwamnan ya bukaci shugabannin kananan hukumomin da su yi koyi da magabatansu wajen mayar da hankali kan shirye-shiryen da suka shafi jama’a, wadanda yawanci gwamnatin jihar ke fara aiwatarwa, domin inganta rayuwar jama’a.

Gwamna Badaru ya bukaci mazauna jiharnan da su bayar da dukkanin hadin kai da goyon bayan da ake bukata ga sabbin ciyamomin domin basu damar samar da romon demokradiyya ga jama’a.

Leave a Reply

%d bloggers like this: