Majalisar Wakilai ta zartar da kudirin dokar inganta masana’antar man fetur.

Kwamitin bai daya na majalisar a yau ya duba rahoton kwamitin wucin gadi akan kudirin dokar inganta masana’antar man fetur tare da zartar da ita.

Shugaban kwamitin wucin gadin, Mohammed Monguno, ya gabatar da rahoton inda ‘yan majalisar suka kada kuri’a akan sassa 319 na kudirin.

Monguno yace bayan zartar da kudirin, majalisa ta tara ta samu nasarar zartar da kudirori masu muhimmanci.

Ya kara da cewa kudirin dokar zai mayar da masana’antar mai da iskar gas ta zama mai gaskiya.

Tsohon shugaban kasa Marigayi Umar Yar’Adua ne ya fara gabatar da kudirin ga majalisun kasa a shekarar 2008.

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya sake gabatar da kudirin ga majalisun kasa a shekarar 2012.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: