Gwamna Jihar Jigawa ya aike da sakon taya murna ga mai martaba sarkin Hadejia bisa cikarsa shekaru 20 akan karagar mulki

0 138

Gwamna Jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar ya aike da sakon taya murna ga mai martaba sarkin Hadejia kuma shugaban majalissar sarakunan jihar Jigawa, Alhaji Dr. Adamu Abubakar Maje CON, bisa cikarsa shekaru 20 akan karagar mulki.

Sakon taya murnar mai dauke dasa hannun mai baiwa gwamna shawara kan kafafan yada labarai da hulda da jama’a, Habibu Nuhu Kila ta bayyana Sarkin a matsayin mai ilmi kuma mai kishin cigaban yankin Hadejia da jihar Jigawa da kuma kasa baki daya.

Gwamna Badaru Abubakar yace mai martaba sarki ya kawo gagarumin cigaba da zaman lafiya a yankin, jiha da kuma kasa baki daya.

Ya bayyana cewa mai martaba sarki yana mara baya ga shirye-shiryen cigaba wadanda ke jawo cigaba da zaman lafiya.

Gwamnan ya yi addu’ar Allah SWT ya karawa Sarki lafiya da kuma karin shekaru masu albarka domin cigaba da hidimtawa al’umma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: