‘Ruwan sama ne yake kawo ambliyar ruwa ba sakin sa daga madatsar ruwa ta Tiga ko Challawa Goje ba’ – Da’u Aliyu

0 117

Hukumar raya kogunan Hadejia-Jama’are ta ta’allaka yawan ambaliyar ruwan da ake yi ga mamakon ruwan sama da ake samu, ba wai sakin ruwa daga madatsar ruwa ta Tiga ko Challawa Goje ba.

Manajan Daraktan Hukumar, Injiniya Ma’amun Da’u Aliyu ya bayyana haka ta cikin wani shirin Radio Jigawa.

Yace manoman da suke karya hanyoyin ruwa da zummar yin noman rani ya taimaka wajen samun ambaliyar ruwa a garuruwan dake gabar Kogin Hadejia-Jama’are.

Injiniya Ma’amun Dau ya gargadi manoma su guji yanka hanyoyin ruwa da zummar yin noman rani ba tare da samun shawarwarin kwararru ba.

Da ya juya ga amfanin madatsun ruwa kuwa, manajan daraktan yace a yanzu haka ana amfani da filayen noman rani mai fadin kadada dubu 16 inda mutane miliyan uku suke cin gajiyarsu a yankin Kadawa.

Haka kuma yace akwai fiye da kadada dubu 6 da 700 da ake amfani dasu a yankin noman rani na Auyo da Hadejia, inda mutane fiye da dubu 6 ke amfana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: