Gwamna Mohammed Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya ce shi da Sanata Danjuma Goje basu da tabbacin kai wa shekarar 2023 a raye

0 71

Gwamna Mohammed Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya ce shi da Sanata Danjuma Goje basu da tabbacin kai wa shekarar 2023 a raye.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yau yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai na fadar shugaban kasa a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne wasu da ake zargin ‘yan bangar siyasa ne suka kai wa ayarin motocin Sanata Goje hari a lokacin da ya je babban birnin jihar domin halartar wani daurin aure.

Mai taimakawa tsohon gwamnan jihar Gombe, Lilian Nworie, a wata sanarwa da ta fitar, ta yi zargin ‘yan bangar da cewa masu biyayya ne ga gwamnan jihar Gombe Inuwa Yahaya.

Goje, wanda ya kai korafi ga babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, ya bukaci a binciki harin da aka kai masa.

Sai dai da yake jawabi a yau, Gwamna Yahaya ya yi alkawarin kawo karshen ayyukan ‘yan Kalare tare da gargadin masu alaka da su, da su daina tun daga yanzu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: