Aranar Talata Gwamna Samuel Ortom na Jihar Binuwe, ya yi wata ganawar sirri da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a fadarsa ta Villa da ke birnin Abuja.

Ganawar na zuwa ne bayan kwanaki kadan da wasu ’yan bindiga suka kai wa Gwamnan hari a karshen makon da ya gabata.

A ranar Asabar ce wasu ’yan bindiga suka kai wa ayarin motocin gwamnan hari yayin da yake dawowa daga wata gonarsa a kauyen Tyomu da ke kan babbar hanyar Makurdi zuwa Gboko.

Bangarori da dama a kasar sun yi ta Allah wadai da wannan harin, inda Shugaban Kasar a ranar Lahadi ya bai wa hukumomin tsaro umarnin gudanar da bincike mai zurfi a kan lamarin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: