Hukumomi a Jamus, sun kara tsawaita dokar kullen corona ganin yadda annobar ke ci gaba da yaduwa a sassan kasar. Matakin na zuwa ne yayin da wasu a Jamus suka fara kosawa.

Jamus ta sake tsawaita dokar kullen corona har zuwa ranar 18 ga watan gobe na Afrilu, matakin da ke nufin tabbatar da tsananta matakan hana yaduwar cutar da har yanzu ta ki lafawa.

Shugabar gwamnati Angela Merkel da sauran jagororin jihohin kasar ne suka cimma wannan matsaya da jijjibin wannan safiya, bayan kwashe sa’o’i 11 suna musayar yawu.

Shugabannin sun amince da daukar tsauraran matakai na musamman a cikin wasu kwanaki biyar a lokacin hutun Easter da ke tafe.

Dukkanin harkoki na hada-hada dai za su kasance a rufe a yayin wa’adin, in banda shagunan sayar da kayan abinci da na magunguna da kuma cibiyoyin gwajin cutar ta corona.

Ana bukatar mazauna Jamus su kasance a gidajensu a kwanakin hutun na Easter, kamar yadda aka haramta duk wasu tarukan da ka iya hada jama’a a lokaci guda.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: