Gwamnan El-Rufai ya jajantawa iyalan wadanda harin ‘yan bindiga ya rutsa da su jihar Kaduna

0 81

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya jajantawa iyalan wadanda harin ‘yan bindiga ya rutsa da su a kananan hukumomin Chikun da Igabi na jihar.

A wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya fitar jiya, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a cocin Emmanuel Baptist dake Kakkau Daji a karamar hukumar Chikun inda aka kashe wani mai ibada tare da sace wasu da ba a tantance adadinsu ba.

Sanarwar ta kuma tabbatar da cewa wani mai ibada ya samu rauni a lamarin.

Sai dai kungiyar kiristoci ta Kasa CAN ta ce sama da mutane 100 ne aka sace a cocin, yayin da kuma ta tabbatar da mutuwar wani mai ibada.

Da yake tofa albarkacin bakinsa, shugaban kungiyar na Kaduna, Joseph Hayab, ya koka kan yadda tsaro ya ta’azzara a jihar, sabanin tabbacin da gwamnati ta bayar.

Kungiyar ta kuma ce ‘yan fashin sun tuntubi iyalan daya daga cikin masu ibadar da aka sace inda suka bukaci a biya su makudan kudin fansa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: