Gwamnan jihar Anambra Willie Obiano da matarsa sun kaɗa ƙuri’arsu a zaɓen gwamnan jihar da akeyi yau
Gwamnan jihar Anambra Willie Obiano da matarsa Ebelechukwu Obiano sun kaɗa ƙuri’arsu a zaɓen gwamnan jihar.
Sun kaɗa ƙuri’a ne a mazaba mai lamba 004 ta makarantar firamari ta Eri.
Ƴan takara 18 ne ke fafatawa a zaɓen gwamnan Anambra
Gwamnan wanda ke kammala wa’adin mulkinsa ya yi kira ga mutanen jihar da suka cancanci kaɗa ƙuri’a su fito su yi zaɓe.
