Gwamnan Jihar Bauchi ya bayyana cewa matakan da gwamnatin tarayya take dauka domin kare rayuka da dukiyoyin yan Najeriya basu gamsar ba

0 29

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya bayyana cewa matakan da gwamnatin tarayya take dauka domin kare rayuka da dukiyoyin yan Najeriya basu gamsar ba, duk da irin kudaden da take kashewa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake kaddamar da rabon Motoci ga Hakiman kananan hukumomin Jihar a ranar Alhamis da yamma.

Haka kuma ya bayyana yadda lamarin tsaron kasar nan ya tabarbare a matsayin abin takaici, inda ya ce yan bindigar sun shigo Jihar sa ta Bauchi.

Bala Muhammad, ya ce uzurin da gwamnatin tarayya take bayarwa domin boye gazawar ta, abu ne wanda yan Najeriya baza su lamunta ba.

Haka kuma ya ce a kwanakin nan anji lamarin yan bindiga a karamar hukumar Zaki ta Jihar.

Kazalika, ya ce matukar gwamnatin tarayya ta gaza biyan bukatun Sarakunan gargajiyar, Gwamnatin Jiha zata inganta Albashin su, domin ganin cewa sun ci gaba da sanya ido akan lamuran da suka shafi tsaron kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: