Labarai

Ceton talakawa ne yasa na bayyana kudurin tsayawa takarar shugaban Kasa a zaben shekarar 2023 mai zuwa – Ministan Sufuri Rotimi Amaechi

Ministan Sufuri na Kasa Chibuike Rotimi Amaechi, ya bayyana kudurin sa na tsayawa takarar shugaban Kasa a zaben shekarar 2023 mai zuwa.

Manema Labarai sun rawaito cewa Amaechi, ya bayyana hakan ne a taron Jam’iyar APC wanda aka gudanar a birnin Port Harcourt na Jihar Rivers.

Amaechi, ya ce ya rike Ministan Sufuri tsawon shekaru 7, ya yi Gwamna shekaru 8 haka kuma ya yi Kakakin Majalisar tsawon shekaru 8.

Haka kuma ya ce sau biyu yanayin Darakta Janar na yakin neman zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, a shekarar 2015, da 2019 inda ya kara da cewa yana da gogewa a fannin ciyar da Kasa gaba.

Ministan ya ce zai yi amfani da gogewarsa wajen ciyar da kasa gaba biyo bayan yadda matsaloli suka dabaibaye kasar nan.

A cewarsa, Shugaba Buhari ya dora kasar a mizanin cigaba wanda zata bunkasar Kasar a nan gaba.

Cikin mutanen da suka sanya Idanu a lokacin kaddamar da takarar sun hada da Gwamnan Plateau Simon Lalong, da tsohon shugaban Jam’iyar APC Comrade Adams Oshiomole, Sanata Ali Ndume, Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai ta Kasa Ahmed Idris Wase, da Karamar Ministar Sufuri Gbemisola Saraki, da kuma tsohon Gwamnan Adamawa Jibrin Bindow.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: