Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya haramta sayar da man fetur a yankin Bama da kewaye a kokarinsa na dakile matsalar tsaro, kamar yadda.
Gwamnan ya bayyana cewa wannan mataki ya biyo bayan shawara da hukumomin tsaro suka bayar domin dakile yaduwar kayan aiki da ke taimaka wa ‘yan ta’adda.
Ya bayyana cewa dokar ta fara aiki nan take, kuma duk wanda aka kama da karya ta, zai fuskanci cikakken hukunci ba tare da la’akari da matsayinsa ba.
Gwamna Zulum ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta yi sassauci ba har sai ya ga an samu zaman lafiya mai ɗorewa a jihar, inda ya bukaci hadin kai daga jama’a don nasarar yaki da ta’addanci.