Gwamnonin Arewa sun shirya wani muhimmin taro da za a gudanar a yau Asabar, 10 ga Mayu, 2025 a Kaduna. Rahotanni sun bayyanna cewa za a yi taron ne domin duba yadda za a shawo kan matsanancin halin rashin tsaro da ke addabar yankin.
Shugaban kungiyar gwamnonin Arewa ne ya kira taron, kamar yadda daraktan yada labaran gidan gwamnatin Gombe, Ismaila Uba Misilli ya tabbatar wa da jaridar Punch.
Misilli ya ce an riga an amince da gudanar da taron, kuma batun tsaro ne a saman jadawalin tattaunawar da za a yi.