Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, Ya Zama Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa

0 72

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya zama shugaban kungiyar gwamnonin jihohin Arewa.

Inuwa Yahaya wanda gwamnonin Arewa 19 ne suka zabe shi yayin taron kungiyar da aka gudanar jiya a Otal din Transcorp Hilton da ke Abuja zai karbi ragamar mulki daga hannun Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato daga ranar 29 ga Mayu, 2023.

A jawabinsa na godiya, Inuwa Yahaya ya yi alkawarin tabbatar da amincewar da takwarorinsa suka yi masa daga jam’iyyu daban-daban.

Ya kuma jaddada cewa zai tabbatar da dorewar kyawawan abubuwan da zai gada a kungiyar domin samar da kyakkyawar makoma ga al’ummar Arewa zuwa karshen wa’adinsa na shugaban kungiyar gwamnonin Arewa.

Inuwa Yahaya ya tabbatarwa da takwarorinsa gwamnonin cewar bisa manufar kafa wannan kungiya, zai yi kokarin ganin ya dore da ci gaban da magabatansa suka bari.

Ya ce a karkashin mulkinsa, kungiyar za ta mayar da hankali ga ci gaban tattalin arziki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: