Tsohon Firay Ministan Burtaniya, Tony Blair, Ya Bayyana Shirinsa Na Marawa Gwamnatin Bola Tinubu Baya

0 126

Tsohon Firay Ministan Burtaniya, Tony Blair, ya bayyana shirinsa na marawa gwamnatin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu baya domin samun nasara a kan karagar mulki.

Wata sanarwa da kakakin zababben shugaban kasar, Abdulaziz Abdulaziz ya fitar, ta ce Tony Blair ya bayar da wannan alkawari ne a jiya a lokacin da ya ziyarci zababben shugaban a fadarsa da ke Abuja.

Ya ce Cibiyar Tony Blair ta Kawo Sauyi a Kasashen Duniya wacce ya assasa, za ta kasance aminiyar gwamnatin Bola Tinubu musamman wajen ba da fifiko ga manufofinta da kuma isar da su.

Ya ce tun bayan da ya bar mulki a matsayinsa na firaministan Burtaniya, ya ke hada kai da gwamnatocin kasashen duniya domin taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu.

Ya yabawa gangamin yakin neman zaben Bola Tinubu da bayar da fifiko kan harkokin tsaro, tattalin arziki, noma da kuma wutar lantarki, inda ya bayyana yadda bangarorin suke tafiya kafada da kafada saboda muhimmancinsu ga ci gaban kowace al’umma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: