A zaman majalisar zartarwa gwamna Inuwa ya amince da bada aikin wasu Tituna da zasu haɓaka rayuwar mutanen dake zaune a yankunan karkara wanda jimillar tsawon su ya kai kilomita 74 da ɗoriya a wasu ƙananan hukumomin jihar Gombe.
Aikin sune kamar haka:-
– Bajoga zuwa Magaba a karamar hukumar Funakaye.
– Daniya zuwa Daban-Fulani a karamar hukumar Kwami
– Dukku zuwa Zange mai tsawon kilomita 31.4 a karamar hukumar Dukku.
– Gelengu zuwa Balanga-Koni zuwa Balanga-Gari mai tsawon kilomita 4.5 a karamar hukumar Balanga.
– Kembu zuwa Kidda zuwa Panda zuwa Garin Alaji Titi mai tsawon kilomita 24.9 a karamar hukumar Akko