Majalisar Dattawa ta amince da dokoki biyu daga cikin manyan dokokin gyaran haraji guda hudu da ke gaban ta, matakin da ke nuna ci gaba wajen gyara tsarin tattara haraji a Najeriya.
Dokokin da aka amince da su sun haɗa da wanda ke neman soke dokar kafa Hukumar Harajin Cikin Gida ta Tarayya (FIRS) da kuma dokar kafa Sabuwar Hukumar Hadin Gwiwar Tara Haraji ta Kasa (Joint Revenue Board Establishment Bill 2025) da kuma dokar kafa Hukumar Harajin Najeriya (Nigeria Revenue Service Bill 2025).
An amince da dokokin ne bayan nazari kai tsaye da aka yi kan kowanne sashe a zaman kwamitin gaba ɗaya na majalisar, sannan aka karanta su karo na uku a zauren majalisa.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne ya mika dokokin hudu ga Majalisar Dokoki a watan Oktoban shekarar 2024 domin tantancewa da amincewa da su.
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya yaba da matakin da aka dauka, inda ya bayyana fatansa cewa dokokin za su inganta shugabanci tare da kawo sauyi a harkar tara haraji da raba shi a fadin ƙasa.