

- Gwamna Zulum ya raba wa likitoci fiye da 80 didaje da kudi Naira miliyan 79 don inganta rayuwarsu - July 2, 2022
- Manyan Sarakunan kasar Yarabawa sunyi kiran samun zaman lafiya daga gwamnati kafin zaben 2023 - July 2, 2022
- Kasar Jamus za ta fara dawo wa da Najeriya dubban kayayyakin tarihin ta da aka wawushe tun lokacin mulkin mallaka - July 2, 2022
Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta sanar da korar malamai 2,356, da suka gaza cin jarrabawar gwaji da aka yi musu.
Hukumar da ke kula da ilimi matakin farko ta KADSUBEB ta sanar da matakin ranar Lahadi, wanda ya shafi har da shugaban kungiyar malamai ta kasa Audu Amba.
Mai magana da yawun KADSUBEB Hauwa Mohammed ta ce hukumar ta yi jarrabawar ne ga sama da malamai 30,000 a cikin watan Disamban 2021.
Ta ce sun kori malaman firamare 2,192 da suka hada da Shugaban kungiyar malamai ta kasa wato NUT, Audu Amba, saboda kin zana jarrabawar kwata-kwata.
Ta kara da cewa sun kori wasu malamai 165 daga 27,662 saboda gaza samun makin da ya dace.
“Ba a bukatar aikin malaman da suka samu maki kasa 40, saboda haka an kore su daga aiki.,” in ji ta.
Sai dai shugaban kungiyar malamai na jihar Kaduna Ibrahim Dalhatu ya yi watsi da jarrabawar, wadda ya ce ba a shirya ta kan ka’ida ba.
Ko a 2018, gwamnatin jihar Kaduna ta kori malamai 21,780 bayan gaza cin jarabawar gwaji, inda daga baya ta dauki wasu 25,000 bayan yi musu gwaji.
-BBCHAUSA