Rundunar yan sandan Jihar Kano ta kama wasu mutane 3 bisa zargin su da hada-hadar takardun motoci na bogi

0 92

Rundunar yan sandan Jihar Kano ta kama wasu mutane 3 bisa zargin su da hada-hadar takardun motoci na bogi.

Kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Kano.

A cewarsa, an kama mutanen wanda suka hada da Odinaka Godwin da kuma wasu mutane 2, inda aka samu Lambar motoci 9 a hannun su da kuma wasu Motoci 10 da suka sace.

Kiyawa, ya bayyana cewa bayan tsananta bincike sun yi nasarar kama Abdulra’uf Olalade dan shekara 57 da Abdullahi Suleman da kuma Suleman Ibrahim.

Haka kuma ya ce mutanen sun amince da laifin su na sayar da takardun bogi ga mutane.

Sanarwar ta ce ana cigaba da tsananta bincike kafin gabatar da mutuman a Kotu.

Kazalika, ya ce an mika motoci 7 daga cikin 10 da aka samu a hannun mutanen ga masu su, inda kuma ake cigaba da bincike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: