Gwamnan Jihar Ribas ya amince da bada ₦100,000 ga kowannne ma’akacin gwamnati a Jihar

0 186

Gwamnan Jihar Ribas Siminalayi Fubara, ya amince da da baiwa kowannne ma’akacin gwamnatin a Jihar dubu 100 a jihar.

Tallafin kudin za’a raba shi ga dubban ma’aikata a kowacce ma’aikatar, sashen ayyuka da hukumomi na Jihar.

Kwamishinan yada labarai na Jihar Mista Joe Johnson yace an amince da fitar da kudin domin ma’aikatan jihar su samu damar gudanar da shagul-gulan sabuwar shekara cikin farin ciki.

Tuni gwamna Fubara, ya bayyana kudirin gwamnatin sa na samar da walwalar ma’akata a jihar. Yayin gabatar da kasafin kudin shekarar 2024 ga majalisar dokokin jihar, gwamnan yayi alkawarin cike gibi da ake samu a bangaran aikin gwamnati tare da daukar ma’aikata a kan lokaci a fadin jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: