Gwamnan jihar Sokoto ya yi kira ga shugaba Buhari da ya sanya dokar ta ɓaci a jihohin da ƴan fashin daji sukayi katutu

0 113

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziru Tambuwal ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sanya dokar ta baci a jihohin da ‘yan fashin daji suke adabbar al’umominsu.

Mai taimakawa Gwamnan na musamman akan kafafen yada labarai Mohammed Bello ne ya bayyana hakan, inda ya ce a ganawar da suka yi da shugaba Buhari a jiya Litinin a Abuja, ya ce gwamna ya fadawa shugaban cewa kundin tsarin mulki ya ba shi damar yin haka.

Ya kara da cewa sanya dokar ta baci zai taimaka wajan kakkabe yan ta’addan dake addabar yankin arewa maso gabashin kasar nan.

Gwamnan Tambuwal ya kuma bukaci a sanya dokar a dukkanin Jihohin Sokoto, Zamfara, Katsina, Kaduna, Niger da Kebbi, domin gudun, tserewar yan ta’addan zuwa wasu dazuka dake makwabtaka.

Ya kuma bukaci shugaban kasa Muhammadu buhari ya tura jami’an tare da kayan yaki na zamani domin magance matsalar rashin tsaro a yankin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: