Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da bada tallafin kayan abinci domin watan Ramadan ga mutane dubu 25

0 87

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da bada tallafin kayan abinci domin watan Ramadan ga mutane dubu 25 da suka hada da marasa galihu da ‘yan gudun hijira a jihar.

Zababben sakataren hukumar agajin gaggawa ta jihar Yobe, Dr. Mohammed Goje, ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar yau a Damaturu, babban birnin jihar.

Muhammad Goje ya kara da cewa gwamnan ya umarci hukumar da ta tsara tare da tabbatar da rabon kayan tallafin kamar yadda ya kamata, ga wadanda aka yi nufin tallafawa a fadin jihar.

A halin da ake ciki, gwamnatin Burtaniya ta bayar da shawarar kauracewa bulaguro zuwa wasu jihoshin Arewa guda 7.

Jihoshin da Burtaniya ta lissafa sun hada da Yobe, Borno, Adamawa, Gombe, Kaduna, Katsina da Zamfara.

Ofishin raya kasashen waje rainon Ingila ne ya bayar da shawarar a wani bayani da ya fitar wanda aka wallafa a shafinsa na internet.

Leave a Reply

%d bloggers like this: