Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi kira ga hukumomin tsaro a jihar Ogun da su kawo karshen kungiyoyin asiri a jihar.

Shugaban kasar ya bayar da umarnin cikin wata sanarwa a jiya bayan ‘yan kungiyar asiri sun kashe sama da mutane 16 cikin kwanaki 10 a jihar.

Fada tsakanin kungiyoyin asirin biyu a jihar ya jawo kisan wani shahararren dan daba mai suna Tommy, tare da wasu mutane 15.

An fara fada tsakanin kungiyoyin asirin biyu a ranar Litinin kuma ya ta’azzara bayan kisan Tommy a makon da ya gabata.

Da kadan-kadan fadan ya shiga sauran yankunan jihar bayan an kashe matasa 8 a karamar hukumar Sagamu da wani mutum guda a karamar hukumar Yewa ta kudu.

Shugaba Buhari wanda ya damu da yawan kashe-kashen, ta bakin kakakinsa Mallam Garba Shehu, ya umarci hukumomin tsaro da su dakile duk wasu ayyuka masu alaka da kungiyoyin asiri.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: