Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya nuna rashin jin dadinsa bisa sace ɗalibai 15

0 169

Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya nuna rashin jin dadinsa bisa sace ɗalibai 15 tare da wasu malamai a kwalejin fasahar noma da dabbobi dake Bakura, kamar yadda manema labarai suka rawaito.

Matawalle, a wata sanarwa da kakakinsa, Yusuf Idris, ya fitar ranar Litinin, yace alhakin gwamnatin jihar ne ta kubutar da su cikin koshin lafiya.

 A cewarsa, gwamnatin jihar ta kara tsaurara tsaro a dukkan makarantun dake faɗin jihar tun bayan sace ɗalibai mata a Jangebe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: