Mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi magana kan makomar mata a Afghanistan ƙarƙashin mulkin Taliban

0 194

Mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Amina Mohammed ta yi magana kan makomar mata a Afghanistan ƙarƙashin mulkin Taliban.

A saƙon da ta wallafa a shafinta na Twitter, tsohuwar ministar muhalli ta Najeriya ta ce shekaru biyu da suka gabata a Afghanistan ta tattauna da shugabannin mata kuma sun gabatar mata da saƙo mai ƙarfi, wanda zai iya samu koma baya ba a halin yanzu ga ci gaban da aka samu na shekara 20 da suka shude.

A cikin saƙonta, Amina Mohammed ta yi kira ga Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres kan tabbatar kare ƴancin matan Afghanistan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: