Gwamnatin Buhari Ta Ƙaro Jiragen Yaƙi Don Gamawa Da Matsalar Tsaro

0 162

Rundunar Sojin Saman Nijeriya (NAF) ta sake sayen sabbin jiragen sama na yaki domin cigaba da murkushe burbushin matsalar tsaro a kasar nan.

A watan Janairun wannan shekara ta 2019 dai NAF din ta bayar da sautin kero mata jiragen yakin daga kasar Russian.

Labarin da muka samu daga majiya mai tushe dai yanzu haka jiragen guda 6 sun iso.

Kuma ana sanya ran sake ƙarasowar wasu daga ƙasar Italiya.

Wasu lokutan mayakan kungiyar Boko Haram na cin karansu babu babbaka a dalilin rashin isassun manyan makamai ga rundunar sojin.

Koda a shekarun baya sai da ƙasar nan ta yi ta neman hanyar mallakar makamai don yakar yan tada kayar bayan amma hakan bai cimma ruwa ba.

Ana sanya rai sabbin jiragen zasu taimaka matuka wajen kai hare-hare da kuma agajin gaggawa kamar na magani ko na abinci ko kuma ɗauki ga mayakan sojin Nijeriya dake bakin daga.

Leave a Reply

%d bloggers like this: